A wajen wannan taron dai da ya gudana a ranar 25 ga watan Nuwamban shekara ta 2020, Gidauniyar MTDI ta raba kayan jinkai ga Mata 100 da lamarin ya shafa.
Haka ma a taron, an samu gabatar da jawabai na karfafawa da fatar alkhairi daga kungiyoyin bayar da tallafi na duniya daban-daban.
Haka ma shugaban Assibitin mata da kananan yara ta Maryam Abacha, ya gabatar da bayani akan cutar yoyon fitsari, ya kuma nuna alakar da ke tsakanin cutar da cin zarafin ‘ya’ya mata.
Ita ma a nata jawabin, matar gwamnan jihar Sokoto, Hajiya Mariya Tambuwal ta gabatar da nata jawabin asali da asasi da kuma fafutukar da Gidauniyar ta ke yi domin ceto wadanda wannan ibtila’i ya farwa.
A bangaren ASATTAHIR kuwa, wanda ya Assasa gidauniyar kuma shugaban amintattu, Mal. Aliyu Sidi Attahiru da Zuwaira Umar Yabo, suka halarci taron.
ASATTAHIR ta halarci taron ne a matsayin abukkiyar hada karfi da karfe da MTDI domin samar da yanayi mai kyau a wannan bangaren.
A taron, da ya kumshi halartar wakilin gwamnan jihar Sokoto, Dr Ali Nname. Sarkin Yakin Gagi Alh. Umar Jabbi, Sa’in Kilgori da dai sauran muhimman al’umma.
an rufe Taron da yin addu’a, da kuma sanar da al’umma shirye-shiryen wayar da kai na kwanaki 16 da aka shirya .

